Karin Magana1hau_bib
1Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.2Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;don ganewa kalmomi masu zurfi;3don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;4don sa marar azanci yă yi hankali,yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,5bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,bari masu tunani kuma su sami jagora,6don su fahimci karin magana da kuma misalai,kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.7Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,amma wawaye sun rena hikima da horo.