Zefaniya3hau_bib

Nan gaba na Urushalima

1Taki ta ƙare, ke birnin mai danniya,mai ’yan tawaye da kuma masu ƙazanta!2Ba kya yi wa kowa biyayya,ba kya kuma yarda da kuskurenki.Ba kya dogara ga Ubangiji,ba kya kuma kusatowa kusa da Allahnki.3Sarakunanki ruri ne na zakoki,shugabanninki kyarketan dare ne,waɗanda ba sa rage kome don safe.4Annabawanki mahaukata nemutanenki masu cin amana ne.Firistocinki suna ƙazantar da Wurin Mai Tsarkisuna kuma keta dokoki.5Ubangiji da yake cikinki mai adalci ne;ba ya yin abin da ba daidai ba.Kowace safiya yakan bayyana dokokinsa a fili,kowace sabuwar rana kuma ba ya kāsawa,duk da haka marasa adalci ba sa jin kunya.6“Na daddatse al’ummai;an kuma rurrushe kagararsu.Na bar titunansu ba kowa,ba mai ratsawa a ciki.An ragargaza biranensu;ba wanda za a bari, babu ko ɗaya.7Na ce wa birnin,‘Tabbatacce za ki ji tsoronaki kuma yarda da gyara!’Ta haka ba za a datse wurin zamanki ba,ba kuwa dukan hukuncena za su hau bisa kansu ba.Amma har yanzu suna marmarisu yi rashin gaskiya a duk abin da suke yi.8Saboda haka ku jira ni,” in ji Ubangiji;“a ranar da zan tsaya in ba da shaida,Na yanke shawara in tattara dukan al’ummai,in tattara mulkokiin kuma zuba fushina a kansu,da dukan zafin haushina.Za a mamaye dukan duniyada zafin fushina.
9“Sa’an nan zan tsarkake leɓunan mutanen,don dukansu su kira bisa ga sunan Ubangijisu kuma yi masa hidima kafaɗa da kafaɗa.10Tun daga ƙetaren rafuffukan Kushmasu yi mini sujada, mutanena da suke a warwatse,za su kawo mini hadayu.11A wannan rana ba za ku sha kunyasaboda laifofin da kuka yi mini,gama zan ɗauke wa wannan birniwaɗanda suke farin ciki cikin girmankansu.Ba kuma za ka ƙara yin kallon renia tuduna mai tsarki ba.12Amma zan zauna a cikinkimasu tawali’u da masu ƙasƙantar da kai,waɗanda suke dogara ga sunan Ubangiji.13Raguwar Isra’ila ba za su ƙara aikata abin da ba daidai ba,ba za su faɗa ƙarya ba,ba kuwa za a sami ruɗu a bakunansu ba.Za su ci su kuma kwantakuma babu wanda zai ba su tsoro.”
14Ki rera, ya Diyar Sihiyona;ki tā da murya, ya Isra’ila!Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki,Ya Diyar Urushalima!15Ubangiji ya ɗauke hukuncinki,ya mai da abokan gābanki baya.Ubangiji, Sarkin Isra’ila, yana tare da ke;ba kuma za ki ƙara jin tsoron wani lahani ba.16A wannan rana za su cewa Urushalima,“Kada ki ji tsoro, ya Sihiyona;kada ki bar hannuwanki su raunana.17Ubangiji Allahnki yana tare da ke,mai iko ne don ceto.Zai yi matuƙar farin ciki da ke,zai rufe ki da ƙaunarsa,zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”
18“Zan cire taƙaici daga gare kia ƙayyadaddun bukukkuwa;su kaya ne da kuma zargi a gare ki.19A wannan lokaci zan jijji wawaɗanda suka danne ku;zan kuɓutar da guraguin kuma tattara waɗanda suke a warwatse.Zan sa a yabe su a kuma girmama sua kowace ƙasar da aka kunyatar da su.20A wannan lokaci zan tattara ku;a wannan lokaci zan kawo ku gida,zan sa a yabe ku a kuma girmama kua cikin dukan mutanen duniyaa sa’ad da na maido da arzikinkua idanunku,”in ji Ubangiji.

No translations available.