Ru’uya ta Yohanna1hau_bib
Gabatarwa
1Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna,2wanda ya shaida dukan abin da ya gani, wato, maganar Allah da kuma shaidar Yesu Kiristi.3Mai albarka ne wanda yake karanta waɗannan kalmomin annabci, masu albarka ne kuma waɗanda suke jinsu, suke kuma sa abin da aka rubuta a ciki a zuciya, domin lokaci ya yi kusa.Gaisuwa da yabo
4Daga Yohanna,Zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai da suke a lardin Asiya.
Alheri da salama gare ku daga shi wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, da kuma daga ruhohi bakwai da suke a gaban kursiyinsa,5da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya.
Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya ’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa,6ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin.7“Duba, yana zuwa cikin gizagizai,kowane ido kuwa zai gan shi,har da waɗanda suka soke shi”;dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.”Bari yă zama haka nan! Amin.8“Ni ne Alfa da kuma Omega,” in ji Ubangiji Allah, “wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, Maɗaukaki.”