Zabura99hau_bib

1Ubangiji yana mulki,bari al’ummai su yi rawan jiki;yana zaune a kursiyi tsakanin kerubobi,bari duniya ta girgiza.2Ubangiji mai girma yana a Sihiyona;an ɗaukaka shi a bisa dukan al’ummai.3Bari mu yabi girmanka da sunanka mai banrazana,shi mai tsarki ne.
4Sarki mai iko ne, yana ƙaunar adalcika kafa gaskiya;a cikin Yaƙub ka yiabin da yake mai adalci da kuma daidai.5Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmuku kuma yi masa sujada a wurin sa ƙafafunsa;shi mai tsarki ne.
6Musa da Haruna suna cikin firistocinsa,Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa;sun kira ga Ubangijiya kuwa amsa musu.7Ya yi magana da su daga ginshiƙin girgije;ya kiyaye farillansa da ƙa’idodin da ya ba su.
8Ya Ubangiji Allahnmu,ka amsa musu;ka kasance wa Isra’ila Allah mai gafartawa,ko da yake ka hukunta ayyukansu marasa kyau.9Ku ɗaukaka Ubangiji Allahnmuku kuma yi sujada a dutsensa mai tsarki,gama Ubangiji Allahnmu mai tsarki ne.