Zabura96hau_bib

1Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji;ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.2Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa;ku yi shelar cetonsa kowace rana.3Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.
4Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo;tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.5Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,amma Ubangiji ne ya yi sammai.6Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.
7Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummaiku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi.8Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa;ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa.9Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa;ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya.10Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.”Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba;zai yi wa mutane hukunci da gaskiya.
11Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa;12bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu.Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;13za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa,yana zuwa don yă hukunta duniya.Zai hukunta duniya cikin adalcimutane kuma cikin amincinsa.