Zabura93hau_bib
1Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka;Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi.An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.2An kafa kursiyin tun da daɗewa;kana nan tun fil azal.3Tekuna sun taso, ya Ubangiji,tekuna sun ta da muryarsu;tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa.4Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye,mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku,Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne.5Ƙa’idodinka suna nan daram;tsarki ya yi wa gidanka adohar kwanaki marar ƙarewa, ya Ubangiji.