Zabura8hau_bib

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.Zabura ta Dawuda.

1Ya Ubangiji, shugabanmu,sunanka da girma take a cikin dukan duniya!Ka kafa ɗaukakarkabisa sammai.2Daga leɓunan yara da jariraika kafa yabo domin su sa abokan gābankada masu ɗaukan fansa su yi shiru.3Sa’ad da na dubi sammai,aikin yatsotsinka,wata da taurariwaɗanda ka ajiye a wurarensu,4wane ne mutum da kake tunawa da shi,ɗan mutum da kake lura da shi?
5Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allahka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.6Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka;ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,7dukan shanu da tumaki,da kuma namun jeji,8tsuntsayen sararin samada kifin teku,da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.
9Ya Ubangiji, shugabanmu,sunanka da girma take a cikin dukan duniya!