Zabura79hau_bib

Zabura ta Asaf.

1Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka;sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki,sun bar Urushalima kufai.2Sun ba da gawawwakin bayinkakamar abinci ga tsuntsayen sararin sama,nama jikin tsarkakanka ga namun jejin duniya.3Sun zubar da jini kamar ruwako’ina a Urushalima,kuma babu wani da zai binne matattu.4Mun zama abin reni ga maƙwabta,abin ba’a da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.
5Har yaushe, ya Ubangiji za ka yi ta fushi? Har abada ne?Har yaushe kishinka zai yi ta ƙuna kamar wuta?6Ka zuba fushinka a kan al’ummanda ba su yarda da kai ba,a kan mulkokinda ba sa kira bisa sunanka;7gama sun cinye Yaƙubsuka lalatar da ƙasar zamansa.
8Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu;bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu,gama mun fid da zuciya sarai.9Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu,saboda ɗaukakar sunanka;ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmusaboda sunanka.10Don me al’ummai za su ce,“Ina Allahnsu yake?”A idanunmu, ka sanar wa al’ummaicewa kana ɗaukan fansar jinin bayinka da aka zubar.11Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka;ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa.12Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwaizage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji.13Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka,za mu yabe ka har abada;daga tsara zuwa tsaraza mu yi ta ba da labarin yabonka.