Zabura60hau_bib

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktamta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayimda Aram-Zoba,da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri.

1Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu;ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!2Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta;ka daure karayarta, gama tana rawa.3Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala;ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.4Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tutadon a buɗe gāba da baka. Sela
5Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama,domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.6Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki,“Da nasara zan rarraba Shekemin kuma auna Kwarin Sukkot.7Gileyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne;Efraim shi ne hular kwanona,Yahuda kuma sandar mulkina.8Mowab shi ne kwanon wankina,a kan Edom zan jefa takalmina;a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”
9Wa zai kawo ni birnin katanga?Wa zai bishe ni zuwa Edom?10Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi muba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?11Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba,gama taimakon mutum banza ne.12Tare da Allah za mu yi nasara,zai kuma tattake abokan gābanmu.