Zabura50hau_bib
Zabura ta Asaf.
1Maɗaukaki, Allah, Ubangiji,ya yi magana ya kuma kira duniyadaga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa.2Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau,Allah na haskakawa.3Allahnmu yana zuwaba kuwa zai yi shiru ba;wuta mai cinyewa a gabansa,babban hadari kuma ya kewaye shi.4Ya kira sammai da suke bisa,da duniya, don yă shari’anta mutanensa.5“Ku tattara mini shafaffuna,waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.”6Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsagama Allah kansa alƙali ne. Sela7“Ku ji, ya mutanena, zan kuwa yi magana,Ya Isra’ila, zan kuwa ba da shaida a kanku.Ni ne Allah, Allahnku.8Ba na tsawata muku saboda hadayunkuko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana.9Ba na bukatan bijimi daga turkenkuko awaki daga garkunanku,10gama kowace dabbar kurmi nawa ne,da kuma shanu a kan dubban tuddai.11Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsukuma halittun filaye nawa ne.12Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba,gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta.13Ina cin naman bijimai neko ina shan jinin awaki ne?14“Ku miƙa hadayar godiya ga Allah,ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,15ku kira gare ni a ranar wahala;zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”16Amma ga mugaye, Allah ya ce,“Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokinako na yin maganar alkawarina a leɓunanku?17Kun ƙi umarninakuka kuma zubar da kalmomina a bayanku18Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi;kukan haɗa kai da mazinata.19Kuna amfani da bakunanku don muguntakuna kuma gyara harshenku don ruɗu.20Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwankuku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku.21Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru;kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne.Amma zan tsawata mukuin kuma zarge ku a fuskarku.22“Ku lura da wannan, ku da kuka manta da Allah,ko kuwa in yayyage ku kucu-kucu, ba kuma wanda zai cece ku.23Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni,ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah.”