Zabura3hau_bib
Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom.
1Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne!Su nawa suke gāba da ni!2Da yawa suna magana a kaina suna cewa,“Allah ba zai cece shi ba.” Sela3Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.4Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela5Na kwanta na yi barci;na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.6Ba zan ji tsoro ko dubu gomasuka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.7Ka tashi Ya Ubangiji!Ka cece ni, ya Allahna!Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi;ka kakkarya haƙoran mugaye.8Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo.Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela