Zabura23hau_bib
Zabura ta Dawuda.
1Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,2Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa,yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya,3yakan maido da raina.Yakan bi da ni a hanyoyin adalcisaboda sunansa.4Ko da na yi tafiyata kwari na inuwar mutuwa,ba zan ji tsoron mugu ba,gama kana tare da ni;bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya,za su yi mini ta’aziyya.5Ka shirya mini tebura gaban abokan gābana.Ka shafe kaina da mai;kwaf nawa ya cika har yana zuba.6Tabbatacce alheri da ƙauna za su bidukan kwanakin raina,zan kuwa zauna a gidan Ubangijihar abada.