Zabura15hau_bib
Zabura ta Dawuda.
1Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka?Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?2Sai wanda ba shi da laifikuma yana yin abin da yake daidai,wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa3ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa,wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa muguntaba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,4wanda yake ƙin mugun mutumamma yakan girmama masu tsoron Ubangiji,yakan cika alkawarinsako da ma ya zafe shi,5wanda yake ba da rance ba tare da ruwa bakuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi.Shi wanda yake yin waɗannan abubuwaba zai taɓa jijjiguwa ba.