Zabura149hau_bib
1Yabi Ubangiji.Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,yabonsa a cikin taron tsarkaka.2Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu;bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.3Bari su yabi sunansa tare da rawasuna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya.4Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa;yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto.5Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirmasu kuma rera don farin ciki a kan gadajensu.6Bari yabon Allah yă kasance a bakunansutakobi mai kaifi kuma a hannuwansu,7don su ɗau fansa a kan al’ummaida kuma hukunci a kan mutane,8don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi,manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe,9don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu.Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa.Yabi Ubangiji.