Zabura131hau_bib

Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

1Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji,idanuna ba sa fariya;ban dami kaina da manyan al’amura bako abubuwan da suka sha ƙarfina.2Amma na haƙura na kuma kwantar da raina;kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa,kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.
3Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangijiyanzu da har abada kuma.