Zabura130hau_bib

Waƙar haurawa.

1Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;2Ya Ubangiji, ka ji muryata.Bari kunnuwanka su sauraraga kukata ta neman jinƙai.
3In kai, ya Ubangiji, za ka lissafta zunubai,Ya Ubangiji, wa zai tsaya?4Amma tare da kai akwai gafartawa,saboda haka ake tsoronka.
5Zan jira Ubangiji, raina zai jira,kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.6Raina na jiran Ubangijifiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya,fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.
7Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji,gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewakuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.8Shi kansa zai fanshi Isra’iladaga dukan zunubansu.

No translations available.