Zabura129hau_bib

Waƙar haurawa.

1Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami,bari Isra’ila yă ce,2sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami,amma ba su yi nasara a kaina ba.3Manoma sun nome bayanasuka yi kunyoyinsu da tsayi.4Amma Ubangiji mai adalci ne;ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.
5Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyonaa juye da su baya da kunya.6Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi,wadda takan bushe kafin tă yi girma;7da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa,balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.8Kada masu wuce su ce,“Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku;muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”