Zabura127hau_bib

Waƙar haurawa. Ta Solomon.

1In ba Ubangiji ne ya gina gida ba,masu gininta suna wahala a banza ne.In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba,masu tsaro suna yin tsaro a banza.2Banza ne ka farka da wurika koma da latti,kana fama don abincin da za ka ci,gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.
3’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,yara lada ne daga gare shi.4Kamar kibiyoyi a hannun jarumihaka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.5Mai albarka ne mutuminda korinsa sun cika da su.Ba za a kunyata su basa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

No translations available.