Zabura1hau_bib

1Mai farin ciki ne mutuminda ba ya aiki da shawarar mugayeko yă yi abin da masu zunubi suke yiko yă zauna tare da masu yin ba’a.2Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,kuma yana ta nazarinta dare da rana.3Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa,wanda yake ba da amfani a daidai lokaciwanda kuma ganyensa ba sa bushewa.Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.
4Ba haka yake da mugaye ba!Su kamar yayi neda iska take kwashewa.5Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba,balle a sami masu zunubi a taron adalai.
6Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa,amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.