Karin Magana6hau_bib

Gargaɗi a kan wawanci

1Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi,in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani,2in maganarka ta taɓa kama ka,ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko,3to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka;da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka,ka tafi ka ƙasƙantar da kanka;ka roƙi maƙwabcinka!4Ka hana kanka barci,ko gyangyaɗi a idanunka ma.5Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta,kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.
6Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!7Ba shi da jagoraba shugaba ko mai mulki,8duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da raniya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.
9Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?Yaushe za ku farka daga barcinku?10Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,ɗan naɗin hannuwa don a huta,11talauci kuwa zai zo kamar ’yan harirashi kuma kamar ɗan fashi.
12Sakare da mutumin banzawanda yana yawo da magana banza a baki,13wanda yake ƙyifce da ido,yana yi alama da ƙafafunsayana kuma nuni da yatsotsinsa,14wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa,kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye15Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya;za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.
16Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,17duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,18zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,19mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

Gargaɗi a kan zina

20Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinkakada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.21Ka ɗaura su a zuciyarka har abada;ka ɗaura su kewaye da wuyanka.22Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka;sa’ad da kake barci, za su lura da kai;sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.23Gama waɗannan umarnai fitila ne,wannan koyarwa haske ne,kuma gyare-gyaren horohanyar rayuwa ce,24suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’adaga sulɓin harshen mace marar aminci.
25Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarkakada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.
26Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta,mazinaciya kuma takan farauci ranka.27Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsaba tare da rigunansa sun ƙone ba?28Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafiba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba?29Haka yake da wanda ya kwana da matar wani;babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci.
30Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi satadon yă ƙosar da yunwarsa sa’ad da yake jin yunwa.31Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwaiko da yake abin zai ci dukan arzikin gidansa.32Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali;duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne.33Dūka da kunya ne za su zama rabonsa,kuma kunyarsa za tă dawwama.
34Gama kishi kan tā da hasalar miji,kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa.35Ba zai karɓi duk wata biya ba;zai ƙi cin hanci, kome yawansu.