Karin Magana22hau_bib
1An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa;tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya.2Mawadaci da matalauci suna da abu guda.Ubangiji ne Mahaliccinsu duka.3Mai basira kan ga damuwa tana zuwa yă nemi mafaka,amma marar azanci kan yi ta tafiya yă kuma sha wahala.4Sauƙinkai da tsoron Ubangijisukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.5A hanyoyin mugu akwai kaya da tarko,amma duk wanda ya kiyaye ransa kan kauce musu.6Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.7Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci,mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne.8Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala,za a kuma hallaka sandar fushinsa.9Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka,gama yakan raba abincinsa da matalauta.10Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje;fitina da zargi kuma za su ƙare.11Duk mai son tsabtar zuciya wanda kuma jawabinsa mai alheri nezai zama aminin sarki.12Idanun Ubangiji na lura da sani,amma yakan ƙi kalmomin marar aminci.13Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!”Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!”14Bakin mazinaciya rami ne mai zurfi;duk wanda yake a ƙarƙashin fushin Ubangiji zai fāɗa a ciki.15Wauta tana da yawa a zuciyar yara,amma sandar horo zai kore ta nesa da su.16Duk wanda yake danne matalauta don yă azurtakuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.