Ƙidaya24hau_bib
1To, da Bala’am ya ga cewa Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra’ila albarka, bai koma wajen sihiri kamar dā ba, amma ya juya fuskarsa wajen hamada.2Da Bala’am ya duba sai ya ga Isra’ila sun yi sansani kabila, kabila, Ruhun Allah kuwa ya sauko masa,3sai ya yi annabcinsa ya ce,“Maganar Bala’am ɗan Beyor,saƙon mutumin da idanunsa ke gani sarai,4maganar mutumin da ya saurari maganar Allah,maganar wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki,mutumin da ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe.5“Ina misalin kyan tentunanka, ya Yaƙub,wuraren zamanka, ya Isra’ila!6“Kamar kwaruruka suke a shimfiɗe,kamar lambu kusa da rafi,kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa,kamar itatuwa al’ul kusa da ruwaye.7Ruwa zai kwararo daga bokitinsu;irinsu za su sami ruwa a yalwace.“Sarkinsu zai fi sarkin Agag;mulkinsu zai ɗaukaka.8“Allah ya fitar da su daga Masar;suna da ƙarfin kutunkun ɓauna.Sun cinye abokan gāban,suka kakkarya ƙasusuwansu;da kibiyoyinsu suka sossoke su.9Kamar zaki sun laɓe sun kwanta,kamar zakanya, wa zai yi ƙarfin hali yă tashe su?“Bari waɗanda suka albarkace ka, su sami albarkawaɗanda kuma suka la’anta ka, su la’antu!”10Fushin Balak ya ƙuna a kan Bala’am. Ya tafa hannunsa, ya ce masa, “Na kira ka don ka la’anta abokan gābana, amma sai ga shi ka sa musu albarka har sau uku.11Yanzu ka bar nan ka tafi gida! Na ce zan sāka maka da lada mai kyau, amma Ubangiji ya hana ka samun ladan.”12Bala’am ya ce wa Balak, “Ban faɗa wa ’yan aikan da ka aiko wurina ba cewa,13‘Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba, kuma dole in faɗa abin da Ubangiji ya ce ne kawai’?14Yanzu zan koma wajen mutanena, amma bari in gargaɗe ka game da abin da mutanen nan za su yi wa mutanenka cikin kwanaki masu zuwa.”