Ƙidaya13hau_bib
Leƙen asirin ƙasar Kan’ana
1Ubangiji ya ce wa Musa,2“Ka aiki waɗansu mutane zuwa ƙasar Kan’ana, wadda nake ba Isra’ilawa. Daga kowace kabila, ka aiki ɗaya daga cikin shugabanninta.”3Saboda haka bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya aike su daga Hamadan Faran. Dukansu kuwa shugabanni ne na Isra’ilawa.4Shugabannin kuwa su ne,Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ruben;5Shafat ɗan Hori, daga kabilar Simeyon;6Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;7Igal ɗan Yusuf, daga kabilar Issakar;8Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Efraim;9daga kabilar Benyamin, Falti ɗan Rafu;10Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zebulun;11Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manasse (wata kabilar Yusuf);12Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan;13Setur ɗan Mika’ilu, daga kabilar Asher;14Nabi ɗan Bofsi, daga kabilar Naftali;15Geyuwel ɗan Maki, daga kabilar Gad.16Waɗannan su ne sunayen mutanen da Musa ya aika su binciki ƙasar. (Sai Musa ya ba Hosheya ɗan Nun, suna Yoshuwa.)17Sa’ad da Musa ya aike su domin su binciki Kan’ana ya ce, “Ku haura, ku ratsa ta Negeb har zuwa ƙasar tudu.18Ku ga yadda ƙasar take, ku ga ko mutanen da suke zama a can ƙarfafa ne, ko raunannu, ko su kima ne, ko kuma suna da yawa.19Wace irin ƙasa ce suke zama a ciki, Mai kyau ce, ko mummuna? Waɗanne irin birane ne suke zama a ciki? Suna da katanga, ko babu?20Yaya ƙasar take? Tana da wadata, ko babu? Akwai itatuwa, ko babu? Ku yi iya ƙoƙarinku ku ɗebo daga cikin albarkar ƙasar ku kawo.” (Lokacin farkon nunan inabi ne.)21Saboda haka suka haura, suka binciki ƙasar daga Hamadan Zin har zuwa Rehob, wajen LeboHamat.22Suka kuma haura ta Negeb, suka iso Hebron, inda Ahiman, da Sheshai, da Talmai, zuriyar Anak, suke zama. (An gina Hebron da shekara bakwai kafin a gina Zowan a Masar.)23Da suka iso Kwarin Eshkol,sai suka yanko reshe guda na nonon inabi tare da ’ya’yansa cunkus. Mutum biyu suka ɗauka shi rataye a sanda a kafaɗarsu, suka haɗa tare da rumman da kuma ɓaure.24Sai aka kira wurin Kwarin Eshkol saboda nonon inabin da suka yi cunkus, wanda Isra’ilawa suka yanko a wurin.25A ƙarshen kwana arba’in sai suka komo daga bincikensu.