Nehemiya12hau_bib
Firistoci da Lawiyawa
1Waɗannan su ne firistoci da Lawiyawa waɗanda suka komo tare da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da kuma Yeshuwa.Serahiya, Irmiya, Ezra,2Amariya, Malluk, Hattush3Shekaniya, Rehum, Meremot,4Iddo, Ginneton, Abiya,5Miyamin, Mowadiya, Bilga,6Shemahiya, Yohiyarib, Yedahiya,7Sallu, Amok, Hilkiya da Yedahiya.
Waɗannan su ne shugabannin firistoci da ’yan’uwansu a kwanakin Yeshuwa.8Lawiyawan su ne Yeshuwa, Binnuyi, Kadmiyel, Sherebiya, Yahuda, da kuma Mattaniya, wanda tare da ’yan’uwansa yake lura da waƙoƙin godiya.9Bakbukiya da Unni, ’yan’uwansu sun tsaya ɗaura da su a hidimomi.10Yeshuwa ne mahaifin Yohiyakim, Yohiyakim shi ne mahaifin Eliyashib, Eliyashib shi ne mahaifin Yohiyada,11Yohiyada shi ne mahaifin Yonatan, Yonatan kuma mahaifin Yadduwa.12A kwanakin Yohiyakim, waɗannan su ne shugabannin iyalan firistoci,
na iyalin Serahiya, Merahiya; na iyalin Irmiya, Hananiya;13na iyalin Ezra, Meshullam; na iyalin Amariya, Yehohanan;14na iyalin Malluk, Yonatan; na iyalin Shebaniya, Yusuf;15na iyalin Harim, Adna; na iyalin Merahiyot, Helkai;16na iyalin Iddo, Zakariya; na iyalin Ginneton, Meshullam;17na iyalin Abiya, Zikri; na iyalin Miniyamin da na Mowadiya, Filtai;18na iyalin Bilga, Shammuwa; na iyalin Shemahiya, Yehonatan;19na iyalin Yohiyarib, Mattenai; na iyalin Yedahiya, Uzzi;20na iyalin Sallu, Kallai; na iyalin Amok, Eber;21na iyalin Hilkiya, Hashabiya; na iyalin Yedahiya, Netanel.22Shugabannin iyalin Lawiyawa a kwanakin Eliyashib, Yohiyada, Yohanan da Yadduwa, da kuma na firistoci, an rubuta su a zamanin mulkin Dariyus mutumin Farisa.23Shugabannin iyali cikin zuriyar Lawi har zuwa lokacin Yohanan ɗan Eliyashib, an rubuta su a cikin littafin tarihi.24Shugabannin Lawiyawa kuwa su ne Hashabiya, Sherebiya, Yeshuwa ɗan Kadmiyel, da ’yan’uwansu, waɗanda suka tsaya ɗaura da su don su yi yabo da kuma godiya, sashe ɗaya kan ba da amsa ga ɗaya sashen, kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.25Mattaniya, Bakbukiya, Obadiya, Meshullam, Talmon da Akkub su ne matsaran ƙofofi waɗanda suka yi tsaron ɗaukan ajiya a ƙofofi.26Sun yi hidima a kwanakin Yohiyakim ɗan Yeshuwa, ɗan Yozadak, kuma a kwanakin Nehemiya gwamna da kuma na Ezra firist da kuma marubuci.