1Ki tattara sojojinki, ya ke birnin mayaƙa,gama an kewaye mu da yaƙi.Za su bugi kumatun mai mulkinIsra’ila da sandar ƙarfe.2“Amma ke, Betlehem ta Efrata,ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki a Yahuda,daga cikinki wani zai zo dominawanda zai yi mulkin Isra’ila,wanda asalinsatun fil azal ne.”3Saboda haka za a yashe Isra’ilahar sai wadda take naƙuda ta haihusauran ’yan’uwansa kuma sun dawosu haɗu da Isra’ilawa.4Zai tsaya yă yi kiwon garkensada ƙarfin Ubangiji,cikin girman sunan Ubangiji Allahnsa.Za su kuma zauna lafiya, gama girmansaza tă kai har ƙarshen duniya.5Zai kuma zama salamarsu.Sa’ad da Assuriyawa suka kawo wa ƙasarmu harisuka tattake kagarunmu,za mu tā da makiyaya bakwai,har ma shugabannin mutane takwas su yi gāba da su.6Za su yi mulkin ƙasar Assuriya da takobi,ƙasar Nimrod kuma da zaran takobi.Zai cece mu daga hannun Assuriyawasa’ad da suka kawo wa ƙasarmu harisuka kuma tattake zuwa cikin iyakokinmu.7Raguwar Yaƙub za tă kasancea tsakiyar mutane masu yawakamar raɓa daga Ubangiji,kamar yayyafi a kan ciyawa,wanda ba ya jiran mutumko kuma yă dakata wa ɗan adam.8Raguwar Yaƙub za tă kasance tare da al’ummai,a cikin mutane masu yawa,kamar zaki a cikin sauran namun jeji,kamar ɗan zaki cikin garken tumaki,wanda yake tattaka yă kuma yi kaca-kaca da su sa’ad da yake ratsa a cikinsu,ba kuwa wanda zai cece su.9Za a ɗaga hannunka cikin nasara a kan abokan gābanka,za a hallaka maƙiyanka duka.10“A wannan rana,” in ji Ubangiji“Zan hallaka dawakanku daga cikinku,in kuma rurrushe kekunan yaƙinku.11Zan hallaka biranen ƙasarkuin yi rugu-rugu da dukan katangunku.12Zan kawar da maitarku,ba za a ƙara yin sihiri ba.13Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙada keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku,nan gaba ba za ku ƙara rusunawa aikin hannuwanku ba.14Zan tumɓuke daga gare ku ginshiƙan Asherankuin kuma rurrushe biranenku.15Zan yi ramuwa cikin fushi da hasalaa kan al’umman da ba su yi mini biyayya ba.”