Mika1hau_bib
1Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.2Ku ji, ya ku mutane duka,ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki,bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku,daga haikalinsa mai tsarki.