Makoki3hau_bib

1Ni ne mutumin da ya ga azabata wurin bulalar fushin Ubangiji.2Ya kore ni, ya sa na yi tafiyaa cikin duhu maimakon a cikin haske;3ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da nisau da sau, dukan yini.
4Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufaya kuma karya ƙasusuwana.5Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye nida baƙin ciki da kuma wahala.6Ya sa na zauna a cikin duhukamar waɗanda suka mutu da jimawa.
7Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba;Ya daure ni da sarƙa mai nauyi.8Ko lokacin da nake kira don neman taimako,ba ya jin addu’ata.9Ya tare hanyata da tubula na duwatsu;ya sa hanyata ta karkace.
10Kamar beyar da take a laɓe tana jira,kamar zaki a ɓoye,11ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da niya bar ni ba taimako.12Ya ja kwarinsaya sa in zama abin baratarsa.
13Ya harbi zuciyatada kibiyoyin kwarinsa.14Na zama abin dariya ga mutanena duka;suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.15Ya cika ni da kayan ɗaciya gundure ni da abinci mai ɗaci.
16Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa;ya tattake ni cikin ƙura.17An hana ni salama;na manta da ko mene ne ake kira wadata.18Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙareda kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.”
19Na tuna da azabata da kuma sintiri,da na yi ta yi da ɗacin rai.20Na tuna su sosai,sai kuma na ji ba daɗi a raina.21Duk da haka na tuna da wannanna kuma sa bege ga nan gaba.
22Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.23Sababbi ne kowace safiya;amincinka kuwa mai girma ne.24Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;saboda haka zan jira shi.”
25Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,ga kuma wanda yake neman shi;26yana da kyau ka jira shirudomin samun ceton Ubangiji.27Yana da kyau mutum yă sha wuyatun yana yaro.
28Bari yă zauna shiru shi kaɗai,gama haka Ubangiji ya sa yă yi.29Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙurakila akwai bege.30Bari yă ba da kumatunsa a mare shi,yă kuma bari a ci masa mutunci.
31Gama Ubangiji ba yayashe mutane har abada.32Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai,ƙaunarsa tana da yawa.33Gama ba haka kawai yake kawo wahalako ɓacin rai ga ’yan adam ba.
34Bai yarda a tattake’yan kurkuku a ƙasa ba,35ko kuma a danne wa mutum hakkinsaa gaban Maɗaukaki,36ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiyaashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?
37Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cikain ba Ubangiji ne ya umarta ba?38Ba daga bakin Maɗaukaki nebala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?39Don mene ne wani mai rai zai yi gunagunisa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?
40Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta,sai mu kuma koma ga Ubangiji.41Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmuga Allah na cikin sama, mu ce,42“Mun yi zunubi mun yi tawayeba ka kuwa gafarta ba.
43“Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu;ka karkashe mu ba tausayi.44Ka rufe kanka da gajimaredon kada addu’armu ta kai wurinka.45Ka mai da mu tarkace da jujia cikin mutane.
46“Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana maganamarar daɗi.47Muna cika da tsoro,da lalatarwa da hallakarwa.”48Hawaye na kwararowa daga idanunadomin an hallaka mutanena.
49Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye,ba hutawa.50Har sai in Ubangiji ya dubadaga sama ya gani.51Abin da nake gani yana kawo mini baƙin cikidomin dukan matan birnina.
52Maƙiyana suna farauta taba dalili kamar tsuntsu.53Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin ramisuka kuma jajjefe ni da duwatsu;54ruwaye suka rufe kaina,sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa.
55Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji,daga rami mai zurfi.56Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwankaka ƙi jin roƙona na neman taimako.”57Ka zo kusa lokacin da na kira ka,kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”
58Ya Ubangiji, ka goyi bayana;ka fanshi raina.59Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba.Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!60Ka ga zurfin ramakonsu,da duk mugun shirin da suke yi mini.
61Ya Ubangiji, ka ji zaginsu,da duka mugun shirin da suke yi mini62Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kaigame da ni duk yini.63Dube su! A zaune ko a tsaye,suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu.
64Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji,domin abin da hannuwansu suka yi.65Ka sa yana ta rufe zuciyarsu,kuma bari la’anarka ta bi su.66Ka fafare su cikin fushika hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji.