Yoshuwa13hau_bib
Ƙasar da ba a riga an ƙwace ba tukuna
1Sa’ad da Yoshuwa ya tsufa, Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi kuma akwai sauran ƙasa mai fāɗi da ba ku riga kun mallaka ba.2“Ga ƙasar da ta rage,“dukan yankunan Filistiyawa da na Geshurawa.3Daga Kogin Shihor a gabashin Masar zuwa sashen Ekron a arewa, dukan wannan ƙasa ana lissafta ta a cikin ƙasar Kan’aniyawa, ko da yake tana a sashen da sarakuna biyar na Filistiyawa na Gaza, Ashdod, Ashkeloniyawa, Gat da Ekron; na Awwiyawa.4Daga wajen kudu kuma, dukan ƙasar Kan’aniyawa ce. Iyakarta a arewa ta fara daga Ara ta Sidoniyawa har zuwa Afek, ta zarce har zuwa iyakar Amoriyawa;5da ƙasar Gebaliyawa; da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba’al-Gad a gindin Dutsen Hermon zuwa Lebo Hamat.6“Dukan mazauna kan yankunan tuddai daga Lebanon zuwa Misrefot Mayim, wato, dukan Sidoniyawa, ni da kaina zan kore su a gaban Isra’ilawa. Ka tabbata ka raba wa Isra’ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka,7ka raba ta tă zama gādo wa kabilu tara da kuma rabin kabilar Manasse.”