Ayuba14hau_bib
1“Mutum haihuwar macekwanakinsa kaɗan ne, kuma cike da wahala.2Yana tasowa kamar fure yana kuma shuɗewa;kamar inuwa, ba ya daɗewa.3Za ka zura ido a kan irin wannan ne?Za ka kawo shi gaba don ka yi masa shari’a?4Wane ne zai iya kawo abin da yake da tsarki daga cikin abu marar tsarki?Babu!5An lissafta kwanakin mutum;ka riga ka ɗibar masa watanni,ka yi masa iyaka, ba zai iya wuce iyakar ba.6Saboda haka ka kawar da kanka daga gare shi,ka rabu da shi har sai ya cika lokacinsa kamar mutumin da aka ɗauki hayarsa.7“Aƙalla itace yana da bege.In an sare shi, zai sāke tsira,zai tohu da kyau.8Ko da jijiyoyin itacen sun tsufa a cikin ƙasakuma kututturensa ya mutu a cikin ƙasa.9Daga ya ji ƙanshin ruwa zai tohuyă yi tsiro kamar shuka.10Amma mutum yana mutuwa a bizne shi;daga ya ja numfashinsa na ƙarshe, shi ke nan.11Kamar yadda ruwa yake bushewa a teku ko a gaɓar rafisai wurin yă bushe,12haka mutum zai kwanta ba zai tashi ba;har sai duniya ta shuɗemutane ba za su farka ba, ba za su tashi daga barcinsu ba.13“Da ma za ka ɓoye ni a cikin kabarika ɓoye ni har sai fushinka ya wuce!In da za ka keɓe mini lokacisa’an nan ka tuna da ni!14In mutum ya mutu, ko zai sāke rayuwa?In haka ne zan daurekwanakin da nake shan wahala har su wuce.15Za ka kira zan kuwa amsa maka;za ka yi marmarin abin da hannunka ya halitta.16Ba shakka a lokacin ne za ka lura da matakainaamma ba za ka kula da zunubaina ba.17Za a daure laifofina a cikin jaka;za ka rufe zunubaina.18“Amma kamar yadda manyan duwatsu suke fāɗuwasu farfashe su kuma gusa daga wurarensu,19yadda ruwa yakan zaizaye duwatsuruwa mai ƙarfi kuma yă kwashe turɓayar ƙasa,haka kake barin mutum ba bege.20Ka sha ƙarfinsa gaba ɗaya, sai ya ɓace,ka sauya yanayinsa ka kuma kore shi.21Ko an martaba ’ya’yansa maza, ba zai sani ba;Ko an wulaƙanta su, ba zai gani ba.22Zafin jikinsa kaɗai yake jiyana kuka wa kansa ne kaɗai.”