Irmiya48hau_bib

Saƙo game da Mowab

1Game da Mowab.
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa,
“Kaito ga Nebo, gama za tă lalace.Kiriyatayim za su kunyata a kuma kame ta;katagar za tă sha kunya ta kuma wargaje.
2Ba za a ƙara yabi Mowab ba;a Heshbon mutane za su shirya mata maƙarƙashiya.‘Zo, mu tafi mu kawo ƙarshe ga wannan al’umma.’Ke kuma, ya Madmen za ki yi shiru;takobi zai fafare ki.3Saurari kuka daga Horonayim,kukan risɓewa mai girma da hallaka.4Za a karye Mowab;ƙanananta za su yi kuka.5Sun haura hanyar zuwa Luhit,suna kuka mai zafi yayinda suke tafiya;a hanyar da ta gangara zuwa Horonayimsuna kuka a kan hallakar da aka ji.6Ku gudu! Ku gudu don tserar da ranku;ku zama kamar kurmi a hamada.7Da yake kun dogara ga ayyukanku da arzikinku,ku ma za a kwashe ku bayi,Kemosh zai tafi bauta,tare da firistocinsa da fadawansa.8Mai hallakarwa zai aukar wa kowane gari,kuma ba wani garin da zai kuɓuta.Kwari zai lalacetudu kuma ya hallaka,domin Ubangiji ya faɗa.9Ku sa gishiri a kan Mowab,gama za tă zama kango;garuruwanta za su zama kufai,ba mazauna a cikinsu.
10“La’ananne ne shi wanda yake sake a yin aikin Ubangiji!La’ananne ne wanda ya janye takobinsa daga zub da jini!
11“Mowab ta kasance cikin kwanciyar rai tun ƙuruciyarta,kamar ruwan inabin da aka bari lis,ba a juya daga tulu zuwa wani tulu baba tă tafi bauta ba.Saboda haka tana da ɗanɗanonta,kuma ƙanshinta bai canja ba.12Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji,“sa’ad da zan aika da mutanen da za su tuntsurar da tuluna,su kuma zubar da ita waje.Za su bar tulunan ba kome a cikisu kuma farfashe tulunanta.13Sa’an nan Mowab za tă ji kunyar Kemosh,yadda gidan Isra’ila ya ji kunyasa’ad da suka dogara ga Betel.
14“Yaya za ku ce, ‘Mu jarumawa ne,mutane masu ƙarfi a yaƙi?’15Mowab za tă hallaka a kuma kai wa garuruwanta hari;samarinta kyawawa za su gangara cikin mayanka,”in ji Sarki, wanda sunansa Ubangiji Maɗaukaki ne.16“Fāɗuwar Mowab ta yi kusa;bala’inta zai auku nan da nan.17Yi kuka saboda ita, dukanku mazaunan kewayenta,duk waɗanda suka san shahararta;ku ce, ‘Dubi yadda sandan sarauta mai iko ya karye,dubi yadda sanda mai daraja ya karye!’
18“Sauko daga darajarkuku zauna a busasshiyar ƙasa,Ya mazaunan Diyar Dibon,gama shi mai hallaka Mowabzai haura a kankuzai kuma lalace biranenku masu kagarai.19Ku tsaya a bakin hanya ku duba,ku da kuke zama a Arower.Ku tambayi mutumin da yake gudu da macen da take tserewa,tambaye su, ‘Me ya faru?’20An kunyata Mowab, gama ta wargaje.Ku yi kuka ku kuma tā da murya!Ku yi shela kusa da Arnoncewa an hallaka Mowab.21Hukunci ya zo wa tudu,zuwa Holon, Yahza da Mefa’at,22zuwa Dibon, Nebo da Bet-Dibilatayim,23zuwa Kiriyatayim, Bet-Gamul da Bet-Meyon,24zuwa Keriyot da Bozrazuwa dukan garuruwan Mowab, nesa da kusa.25An karye ƙahon Mowab;an karye hannunta,”in ji Ubangiji.
26“Ku bugar da itadomin ta tayar wa Ubangiji.Bari Mowab tă yi ta birgima a cikin amanta;bari tă zama abin dariya.27Isra’ila ma bai zama abin dariya a gare ki ba?Ba a kama shi cikin ɓarayi,har kaɗa kai na ba’a kike yia duka sa’ad da kike magana game da shi?28Ku bar garuruwanku ku zauna a cikin duwatsu,ku da kuke zama a Mowab.Ku zama kamar kurciyar da take sheƙartaa bakin kogo.
29“Mun ji labarin girman kan Mowabmun ji alfarma girmankanta da kumburintagirmankanta da fariyartada renin zuciyarta.30Na san alfarmanta amma a banza ne,” in ji Ubangiji,“kuma taƙamarta ba ya cimma kome.31Saboda haka zan yi kuka a kan Mowabgama dukan Mowab zan yi kuka,Zan yi gurnani don mutanen Kir Hareset.32Zan yi kuka saboda kai, yadda Yazer ya yi kukaYa kuringar Sibma.Rassanki sun kai har teku;sun kai har tekun Yazer.Mai hallakarwa ya fāɗoa kan ’ya’yan itatuwanku da kuma inabinku da suka nuna.33Farin ciki da murna su ɓacedaga lambunan itatuwa da kuma gonakin Mowab.Na dakatar da malalar ruwan inabi daga wurin matsi;ba wanda zai matse su da ihun farin ciki.Ko da yake akwai sowasowar ba ta farin ciki ba ce.
34“Muryar kukansu na tashidaga Heshbon zuwa Eleyale da Yahaz,daga Zowar har zuwa Horonayim da Eglat Shelishiya,gama har ruwan Nimrim ma sun bushe.35A Mowab zan kawo ƙarshenwaɗanda suke miƙa hadayu a masujadan kan tudusuna kuma ƙone turare ga allolinsu,”in ji Ubangiji.36“Saboda haka zuciyata na makoki don Mowab kamar busa;tana makoki kamar busa saboda mutanen Kir Hareset.Arzikin da suka samu ta ƙare.37An aske kowane kaiaka kuma yanke kowane gemuaka kuma sa wa kowane kwankwaso rigar makoki.38A kan dukan rufi a Mowabda kuma a dandalin jama’ababu wani abu sai kukagama na karye Mowabkamar tulun da babu mai so,”in ji Ubangiji.39“Duba yadda aka ragargazar ta ita! Duba yadda suke kuka!Duba yadda Mowab ta juya bayanta da kunya!Mowab ta zama abin ba’aabin tsoro ga dukan waɗanda suke kewaye da ita.”40Ga abin da Ubangiji yana cewa,“Ga shi! Gaggafa tana firiya zuwa ƙasa,tana shimfiɗa fikafikanta a kan Mowab.41Za a ci Keriyota kuma kame kagarai.A wannan rana zukatan jarumawan Mowabza su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.42Za a hallakar da Mowab a matsayin al’ummadomin ta tayar wa Ubangiji.43Razana da rami da tarko suna jiranku,Ya mutanen Mowab,”in ji Ubangiji.44“Duk wanda ya gudu daga razanazai fāɗa cikin rami,duk wanda ya haura daga ramizai fāɗa cikin tarko;gama zan kawo wa Mowabshekarar hukuncinta,”in ji Ubangiji.
45“A ƙarƙashin Heshbonmasu gudun hijira suna tsaye ba mai taimako,gama wuta ta mutu daga Heshbon,harshen wuta daga tsakiyar Sihon;ta ƙone goshin Mowab,ƙoƙon kai na ’yan tayarwa masu surutu.46Kaitonki, ya Mowab!Mutanen Kemosh sun hallaka;an kai ’ya’yanki maza daurin talala’ya’yanki mata zaman bauta.
47“Duk da haka zan maido da wadatar Mowaba kwanaki masu zuwa,”in ji Ubangiji.A nan hukuncin Mowab ya ƙare.