Irmiya47hau_bib
Saƙo game da Filistiyawa
1Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza.2Ga abin da Ubangiji yana cewa,“Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa;za su zama kogi mai rigyawa.Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta,garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu.Mutane za su yi kuka;dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa3da jin motsin takawar kofatan dawakai,da jin surutun kekunan yaƙin abokin gābada motsin ƙafafunsu.Ubanni ba za su juye don su taimaki ’ya’yansu ba;hannuwansu za su yi laƙwas.4Gama rana ta zoda za a hallaka Filistiyawaa kuma datse dukan waɗanda suka raguwaɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon.Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa,raguwa daga bakin tekun Kaftor.5Gaza za tă aske kanta cikin baƙin ciki;Ashkelon zai yi shiru.Ya raguwar da suke zama a fili,har yaushe za ku tsattsage kanku?6“Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangijisai yaushe za ka huta?Ka koma kubenka;ka huta, ka yi shiru.’7Amma ta yaya zai hutasa’ad da Ubangiji ya umarta,sa’ad da ya umarta shidon yă faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?”No translations available.