1Abubuwan da Allah ya yi magana a kai game da Babilon da Ishaya ɗan Amoz ya gani.2A tā da tuta a kan tudun da yake mai fili,ka tā da murya gare su;ka ɗaga hannu ka ba su alamadon su shiga ƙofofi masu alfarma.3Na umarci tsarkakana;na umarci jarumawan yaƙina su gamsar da fushina,waɗanda suke farin ciki a nasarata.4Ka saurara, akwai surutu a kan duwatsu,sai ka ce na babban taron jama’a!Ka saurara, akwai hayaniya a cikin mulkoki,sai ka ce al’ummai ne suna ta tattaruwa!Ubangiji Maɗaukaki yana shiryamayaƙa don yaƙi.5Suna zuwa daga ƙasashe masu nesa,daga iyakokin duniya,Ubangiji da kuma fushinsa,zai hallaka dukan ƙasar.6Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusaza tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki.7Saboda wannan, hannun kowane mutum zai yi rauni,ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.8Tsoro zai kama su,zafi da azaba za su ci ƙarfinsu;za su yi ta murɗewa kamar mace mai naƙuda.Za su dubi juna a tsorace,fuskokinsu a ɓace.9Duba, ranar Ubangiji tana zuwa,muguwar rana, mai hasala da zafin fushi,don ta mai da ƙasar kangota kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta.10Taurarin sama da ƙungiyoyinsuba za su ba da haskensu ba.Rana za tă yi duhuwata kuma ba zai ba da haskensa ba.11Zan hukunta duniya saboda muguntarta,mugaye saboda zunubansu.Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙamain kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.12Zan sa mutum yă fi zinariya zalla wuyar samuwa,fiye da zinariyar Ofir wuyan gani.13Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki;duniya kuma za tă girgiza daga inda takea fushin Ubangiji Maɗaukaki,a ranar fushinsa mai ƙuna.14Kamar barewar da ake farautartakamar tumaki marasa makiyayi,haka nan kowane mutum zai koma ga mutanensa,kowane mutum zai gudu zuwa ƙasarsa.15Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu;dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi.16Za a fyaɗa ’ya’yansu a ƙasa su yi kucu-kucu a idanunsu;za a washe gidajensu, a kuma kwana da matansu.17Duba, zan zuga mutanen Medes su yi gāba da su,su da ba su kula da azurfa bakuma ba sa damuwa da zinariya.18Bakkunansu za su kashe samari;ba za su ji tausayin jarirai baba za su kuwa nuna jinƙai ga ’yan yara ba.19Babilon, kayan daraja na mulkoki,abin fariyar Babiloniyawa,Allah zai kaɓantar da itakamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra.20Ba za ƙara kasance da mazauna kuma bako a yi zama a cikinta dukan zamanai;Ba wani mutumin Arab da zai kafa tentinsa a can,ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.21Amma halittun hamada za su kwanta a can,diloli za su cika gidajenta;a can mujiyoyi za su zauna,a can kuma awakin jeji za su yi ta tsalle.22Kuraye za su yi ta kuka a kagarorinta,diloli kuma a cikin fadodinta masu alfarma.Lokacinta ya yi kusa,kwanakinta kuma ba za su yi tsawo ba.