1Toho zai fito daga kututturen Yesse;daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya.2Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa,Ruhun hikima da na fahimta,Ruhun shawara da na iko,Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,3zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji.Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba,ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;4amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a,da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya.Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa;da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.5Adalci ne zai zama abin ɗamararsaaminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.6Kyarkeci zai zauna tare da ɗan ragodamisa za tă kwanta tare da akuya,ɗan maraƙi da zaki da ɗan saniya za su yi kiwo tare;ɗan yaro ne zai lura da su.7Saniya da beyar za su yi kiwo tare,ƙananansu za su kwanta tare,zaki kuma zai ci ciyawa kamar saniya.8Jariri zai yi wasa kurkusa da ramin gamsheƙa,ɗan yaro kuma zai sa hannunsa a ramin maciji mai mugun dafi.9Ba za su yi lahani ko su hallakawani a dutsena mai tsarki ba,gama duniya za tă cika da sanin Ubangijikamar yadda ruwaye suka rufe teku.10A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja.11A wannan rana Ubangiji zai miƙa hannunsa sau na biyu don yă maido da raguwar da ta rage na mutanensa daga Assuriya, daga Masar ta Ƙasa, daga Masar ta Bisa,daga Kush,daga Elam, daga Babiloniya,daga Hamat da kuma daga tsibiran teku.12Zai tā da tuta saboda al’ummaiyă kuma tattara masu zaman bauta na Isra’ila;zai tattara mutanen Yahuda da suke a warwatsekusurwoyi huɗu na duniya.13Kishin Efraim zai ɓace,za a kuma kau da abokan gāban Yahuda;Efraim ba zai yi kishin Yahuda ba,haka ma Yahuda ba zai yi gāba da Efraim ba.14Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma;tare za su washe mutane wajen gabas.Za su ɗibiya hannuwa a kan Edom da Mowab,Ammonawa kuma za su yi musu biyayya.15Ubangiji zai busar dabakin tekun Masar;da iska mai zafi zai share hannunsaa bisa Kogin YuferitesZai rarraba shi yă zama ƙanana rafuffuka bakwaisaboda mutane su iya hayewa da ƙafa.16Za a yi babbar hanya saboda raguwa mutanensada ta rage daga Assuriya,kamar yadda ta kasance wa Isra’ilasa’ad da suka fito daga Masar.