1“Ka sa kakaki a leɓunanka!Gaggafa tana a bisan gidan Ubangijidomin mutane sun tā da alkawarinasuka kuma tayar wa dokata.2Isra’ila ta yi mini kuka,‘Ya Allahnmu, mun yarda da kai!’3Amma Isra’ila sun ƙi abin da yake mai kyau;abokin gāba zai fafare su.4Suna naɗa sarakuna, ba da izinina ba;sun zaɓa shugabanni ba da yardanta ba.Da azurfa da zinariyasun ƙera gumaka wa kansuwanda zai kai zuwa ga hallakarsu.5Ku zubar da gunkin maraƙinku, ya Samariya!Fushina yana ƙuna a kansu.Sai yaushe za su rabu da gumaka?6Su daga Isra’ila ne!Wannan maraƙi, mai aikin hannu ne ya yi shi;gunki ne ba Allah ba.Za a farfashe shi kucu-kucu,waccan maraƙin Samariya.7“Gama sun shuka iskadon haka za su girbe guguwa.Hatsin da yake tsaye ba shi da kai,ba zai yi tsaba ba.Ko da ya yi tsaba ma,baƙi ne za su ci.8An haɗiye Isra’ila;yanzu tana cikin al’ummaikamar abin da ba shi da amfani.9Gama sun haura zuwa Assuriyakamar jakin jejin da yake yawo shi kaɗai.Efraim ya sayar da kansa ga maza.10Ko da yake sun sayar da kansu a cikin al’ummai,yanzu zan tattara su wuri ɗaya.Za su fara lalacewaa ƙarƙashi danniyar babban sarki.11“Ko da yake Efraim ya gina bagadai masu yawa don hadayun zunubi,waɗannan sun zama bagade don yin zunubi.12Na rubuta musu abubuwa masu yawa na dokata,amma suka ɗauke su tamƙar wani baƙon abu ne.13Suna miƙa hadayun da aka ba nisu kuma ci nama,amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu.Yanzu zai tuna da muguntarsuyă kuma hukunta zunubansu.Za su koma Masar.14Isra’ila ya manta da Mahaliccinsaya kuma gina fadodi;Yahuda ya gina katanga a yawancin garuruwansa.Amma zan aiko da wuta a bisa biranensuda zai cinye kagaransu.”