HOS7hau_bib
1a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila,zunuban Efraim za su tonuza a kuma bayyana laifofin Samariya.Suna ruɗu,ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje,’yan fashi sukan yi fashi a tituna;2amma ba su ganecewa na tuna da dukan ayyukan muguntarsu ba.Zunubansu sun kewaye su;kullum suna a gabana.3“Suna faranta wa sarki zuciya da muguntarsu,shugabanni kuma da ƙarairayinsu.4Dukansu mazinata nesuna ƙuna kamar matoyawadda mai gashin burodi ba ya bukata yă tura mata wutadaga cuɗe kullu har kumburinsa.5A ranar bikin sarkinmushugabanni sukan bugu da ruwan inabi,yă yi cuɗanya da masu ba’a.6Zukatansu suna kamar matoya;sukan kusace shi da wayo.Muguwar aniyarsu takan yi ta ci dukan dare;da safe sai ta ƙuna kamar harshen wuta.7Dukansu suna da zafi kamar matoya;suna kashe masu mulkinsu.Dukan sarakunansu sukan fāɗi,kuma babu waninsu da yake kira gare ni.8“Efraim yana cuɗanya da al’ummai;Efraim waina ne mai fāɗi da ba a juye ba.9Baƙi sun tsotse ƙarfinsa,amma bai gane ba.Gashi kansa ya cika da furfura,amma bai lura ba.10Girmankan Isra’ila ya ba da shaida a kansa,amma duk da hakabai dawo ga Ubangiji Allahnsako yă neme shi ba.11“Efraim yana kama da kurciya,marar wayo, marar hankali,yanzu yana kira ga Masar,yanzu yana juyewa ga Assuriya.12Sa’ad da suka tafi, zan jefa ragata a kansu;zai janye su ƙasa kamar tsuntsayen sararin sama.Sa’ad da na ji suna tafiya tare,zan kama su.13Kaitonsu,domin sun kauce daga gare ni!Hallaka za tă aukar musu,domin sun tayar mini!Na ƙudura in cece suamma suna faɗar ƙarya a kaina.14Ba sa yin mini kuka da zuciyarsuamma suna ihu a kan gadajensu.Sukan taru wurin ɗaya don hatsi da ruwan inabiamma su juya mini baya.15Na horar da su na kuma ƙarfafa su,amma sun ƙulla mini maƙarƙashiya.16Ba sa juya ga Mafi Ɗaukaka;suna kama da tanƙwararren baka.Za a kashe shugabanninsu da takobisaboda banzan maganganunsu.Saboda wannan za a wulaƙanta sua ƙasar Masar.