Hosiya12hau_bib

1Efraim yana kiwo a kan iska;yana fafarar iskar gabas dukan yiniyana riɓaɓɓanya ƙarairayi da rikici.Ya yi yarjejjeniya da Assuriyaya kuma aika wa Masar man zaitun.2Ubangiji yana da ƙarar da zai kawo a kan Yahuda;zai hukunta Yaƙub bisa ga hanyoyinsazai sāka masa bisa ga ayyukansa.3A cikin mahaifa ya cafke ɗiɗɗigen ɗan’uwansa;a matsayin mutum ya yi kokawa da Allah.4Ya yi kokawa da mala’ika ya kuma rinjaye shi;ya yi kuka ya kuma yi roƙo don tagomashi.Ya same shi a Betelya kuma yi magana da shi a can,5Ubangiji Allah Maɗaukaki,Ubangiji ne sunansa sananne!6Amma dole ku koma ga Allahnku;ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya,ku kuma saurari Allahnku kullum.
7Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya;yana jin daɗin cuta.8Efraim yana fariya yana cewa,“Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta.Da dukan wadatata ba za a samiwani laifi ko zunubi a gare ni ba.”
9“Ni ne Ubangiji Allahnku,wanda ya fitar da ku daga Masar;zan sa ku sāke zauna a tentuna,kamar a kwanakin ƙayyadaddun bukukkuwanku.10Na yi magana da annabawa,na ba su wahayi da yawana kuma ba da misalai ta wurinsu.”
11Gileyad mugu ne?Mutanensa mutanen banza ne!Suna miƙa bijimai a Gilgal?Bagadansu za su zama tsibin duwatsu.A gonar da aka nome.12Yaƙub ya gudu zuwa ƙasar Aram;Isra’ila ya yi bauta don yă sami mata,domin kuma yă biya, sai da ya yi kiwon tumaki.13Ubangiji ya yi amfani da annabi don yă fitar da Isra’ila daga Masarta wurin annabi ya lura da shi.14Amma Efraim ya yi muguwar tsokana da ta sa ya yi fushi;shugabansa zai ɗora musu hakkin jini a kansakuma zai sāka masa saboda wulaƙancinsa.