Hosiya10hau_bib
1Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa;ya fitar da ’ya’ya wa kansa.Yayinda ’ya’yan suka ƙaru,ya gina ƙarin bagadai;da ƙasarsa ta wadata,ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado.2Zuciyarsu masu ruɗu ne,yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu.Ubangiji zai rushe bagadansuyă kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu.3Sa’an nan za su ce, “Ba mu da sarkidomin ba mu girmama Ubangiji ba.Amma ko da ma muna da sarki,me zai yi mana?”4Sun yi alkawura masu yawa,suka yi rantsuwar ƙaryada kuma yarjejjeniyoyi;saboda haka ƙararraki suka tasokamar ciyayi masu dafi da aka nome a gona.5Mutanen da suke zama a Samariya suna tsorosaboda gunki maraƙin Bet-Awen.Mutanensa za su yi makokinsa,haka ma firistocinsa matsafa,waɗanda suka yi farin ciki a kan darajarsa,don an ɗauke ta daga gare su aka kai ta zaman bauta.6Za a ɗauke shi a kai Assuriyakamar gandu wa babban sarki.Efraim zai sha kunya;Isra’ila zai sha kunya saboda gumakan itacensa.7Samariya da sarkinta za su ɓacekamar kumfa a bisa ruwaye.8Za a hallaka masujadai kan tudu na muguntazunubin Isra’ila ne.Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girmasu rufe bagadansu.Sa’an nan za su ce wa duwatsu, “Ku rufe mu!”Ga tuddai kuma, “Ku fāɗo a kanmu!”9“Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra’ila,a can kuwa kuka ci gaba.Yaƙi bai cimmamasu aikata mugunta a Gibeya ba?10Sa’ad da na ga dama, zan hukunta su;al’ummai za su taru su yi gāba da sudon su daure su saboda zunubansu da suka riɓanya.11Efraim horarriyar karsana cemai son sussuka;saboda haka zan sa karkiyaa kyakkyawan wuyanta.Zan bi da Efraim,Dole Yahuda yă yi noma,dole kuma Yaƙub yă ja garman noma.12Ku shuka wa kanku adalci,ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa,ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba;gama lokaci ne na neman Ubangiji,sai ya zoya zubo adalci a kanku.13Amma kun shuka mugunta,kuka girbe mugukuka ci ’ya’yan ruɗu.Domin kun dogara da ƙarfinkuda kuma a jarumawanku masu yawa,14hayaniyar yaƙi za tă tashi gāba da mutanenku,saboda a ragargaza kagaranku,kamar yadda Shalman ya ragargaza Bet-Arbel a ranar yaƙi,sa’ad da aka fyaɗa uwaye tare da ’ya’yansu da ƙasa.15Haka zai faru da kai, ya Betel,domin muguntarka ta yi yawa.Sa’ad da wannan rana ta zo,za a hallaka sarkin Isra’ila ƙaƙaf.