HEB6hau_bib
1Dole mu yi ƙoƙarin zama balagaggu mu kuma fara tunani game da abubuwan da suka fi koyarwan nan mai sauƙi game da Kiristi. Bai kamata mu ci gaba da magana game da me ya sa dole mu juye daga ayyukan da suke kawo mutuwa da kuma me ya sa za mu kasance da bangaskiya a cikin Allah ba.2Kuma bai kamata mu ci gaba da koyar da umarnai game da baftisma, ɗibiya hannuwa, tashin matattu, da kuma madawwamin hukunci ba.3Da yardar Allah, za mu ci gaba ga ƙarin ganewa.4Waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta ta sama, waɗanda suka sami rabo cikin Ruhu Mai Tsarki,5waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa,6ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jama’a.7Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah.8Amma ƙasar da take ba da ƙaya da sarƙaƙƙiya ba ta da amfani tana kuma cikin hatsarin la’ana. A ƙarshe za a ƙone ta.9Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi.10Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba.11Muna so kowannenku yă nuna ƙwazon nan har zuwa ƙarshe, domin ku tabbatar da begenku.12Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari.