Farawa49hau_bib

Yaƙub ya albarkaci ’ya’yansa maza

1Sai Yaƙub ya kira ’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.2“Ku tattaru, ku saurara, ’ya’yan Yaƙub maza;ku saurari mahaifinku, Isra’ila.
3“Ruben, kai ne ɗan farina,ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina,mafi matsayi, kuma mafi iko.4Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba,gama ka hau gadon mahaifinkaka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.
5“Simeyon da Lawi ’yan’uwa ne,takubansu makamai ne na tā da hankali.6Ba zan shiga shawararsu ba,ba zan shiga taronsu ba,gama sun kashe maza cikin fushinsucikin ganin dama suka kashe bijimai.7La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai,hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai!Zan warwatsa su cikin Yaƙubin kuma daidaita su cikin Isra’ila.
8“Yahuda, ’yan’uwanka za su yabe ka;hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka,’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.9Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda,ka dawo daga farauta, ɗana.Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe,kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?10Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba,ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba,sai ya zo ga wanda yake mai shi .Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.11Zai daure jakinsa a kuringa,aholakinsa a rassa mafi kyau;zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabirigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.12Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi,haƙorarsa farare kamar madara.
13“Zebulun zai zauna a bakin teku,yă zama tasar jiragen ruwa;iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon.
14“Issakar doki mai ƙarfi,kwance tsakanin buhunan sirdi.15Sa’ad da ya ga yadda wurin hutunsa yana da kyauda kuma daɗin da ƙasarsa take,zan tanƙware kafaɗarsa ga nauyiyă miƙa kai ga aikin dole.
16“Dan zai tanada adalci wa mutanensakamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila.17Dan zai zama maciji a gefen hanya,kububuwa a bakin hanya,da take saran ɗiɗɗigen dokidomin mahayinsa yă fāɗi da baya.
18“Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.
19“Masu fashi za su fāɗa wa Gad,amma zai runtume su.
20“Abincin Asher zai zama a wadace,zai yi tanadin abinci iri-iri da suka dace don sarki.
21“Naftali sakakkiyar barewa ceda take haihuwar kyawawan ’ya’ya.
22“Yusuf kuringa ce mai ba da amfani.Kuringa mai ba da amfani kusa da rafiwadda rassanta na hawan bango.23Da ɗaci rai mahara suka fāɗa masa;suka harbe shi babu tausayi.24Amma bakansa yana nan daramhannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwasaboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub,saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila,25saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka,saboda Maɗaukaki, wanda yake albarkace kada albarkar sama da take bisaalbarkun zurfafa da suke ƙarƙashin ƙasaalbarkun mama da kuma mahaifa.26Albarkun mahaifi suna da girma fiyeda albarkun daɗaɗɗun duwatsufiye da yalwar madawwaman tuddai.Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf,a goshin ɗan sarki a cikin ’yan’uwansa.
27“Benyamin kyarkeci ne mai kisa;da safe yakan cinye abin da ya farautoda yamma yakan raba ganima.”28Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi.

Mutuwar Yaƙub

29Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti,30kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti.31A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu.32Filin tare da kogon da yake ciki, an saya daga Hittiyawa.”33Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga ’ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa.