Galatiyawa1hau_bib
1Bulus manzo, aikakke ba daga wurin mutum ba, ba kuma ta wurin mutane ba, amma ta wurin Yesu Kiristi da kuma Allah Uba, wanda ya tā da Yesu daga matattu.2Dukan ’yan’uwan kuma da suke tare da ni a nan,
Suna gai da ikkilisiyoyi a Galatiya.3Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.4Shi wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu don yă cece mu daga wannan mugun zamani na yanzu, bisa ga nufin Allah wanda yake kuma Ubanmu,5a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.