1“Ka yi makoki game da sarakunan Isra’ila2ka ce,“ ‘Mahaifiyarki zakanya cecikin zakoki!Takan kwanta cikin ’yan zakokita kuma yi renon kwiyakwiyanta.3Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta,ya yi girma ya zama zaki mai ƙarfi.Ya koyi yayyage abin da ya yi farautayakan kuma cinye mutane.4Al’ummai suka ji labarinsa,aka kuma kama shi cikin raminsu.Suka ja shi da ƙugiyoyizuwa ƙasar Masar.5“ ‘Sa’ad da ta ga sa zuciyarta bai cika ba,abin da take fata gani ya tafi,sai ta ɗauki wani daga cikin kwiyakwiyantata mai da shi zaki mai ƙarfi.6Ya yi ta yawo a cikin zakoki,gama yanzu shi zaki ne mai ƙarfi.Ya koyi yayyage abin da ya yi farautayakan kuma cinye mutane.7Ya rurrushe kagaransuya kuma ragargaza biranensu.Ƙasar da dukan waɗanda suke cikintasun tsorata da jin rurinsa.8Sai al’ummai suka tayar masa,waɗannan daga yankunan da suke kewaye.Suka yafa raga dominsaya kuwa fāɗa cikin raminsu.9Da ƙugiyoyi suka ja shi cikin kejisuka kawo shi wurin sarkin Babilon.Suka sa shi cikin kurkuku,saboda haka ba a ƙara jin rurinsaa kan duwatsun Isra’ila ba.10“ ‘Mahaifiyarku kamar kuringa ce a cikin gonar inabida aka shuka kusa da ruwa;ta ba da ’ya’ya da kuma cikakkun rassasaboda yalwan ruwa.11Rassanta suka yi ƙarfi,suka dace da sandar mai mulki.Ta yi tsayizuwa samaana ganin ta saboda tsayintada kuma saboda yawan rassanta.12Amma aka tumɓuke ta cikin fushiaka jefar da ita a ƙasa.Iskar gabas ta sa ta yanƙwane,aka kakkaɓe ’ya’yanta;rassanta masu ƙarfi suka bushewuta kuma ta cinye su.13Yanzu an shuka ta a hamada,a busasshiyar ƙasa marar ruwa.14Wuta ta fito daga jikin rassantata cinye ’ya’yanta.Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kantada ya dace da sandar mai mulki.’Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.”