Amos3hau_bib

An kira shaidu a kan Isra’ila

1Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar.2“Ku ne kaɗai na zaɓacikin dukan al’umman duniya;saboda haka zan hukunta kusaboda dukan zunubanku.”
3Mutum biyu za su iya yin tafiya tarein ba su yarda su yi haka ba?4Zaki yakan yi ruri a jejiin bai sami kama nama ba?Zai yi gurnani a cikin kogonsain bai kama kome ba?5Tsuntsu yakan fāɗa a tarko a ƙasainda ba a sa tarko ba,ko tarko yakan zargu daga ƙasain ba abin da ya taɓa shi?6Idan aka busa ƙaho a ciki birnimutane ba sa yin rawar jiki?Sa’ad da bala’i ya auko wa birni,ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba?
7Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abuba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.
8Zaki ya yi ruri,wa ba zai tsorata ba?Ubangiji Mai Iko Duka ya yi magana,wa ba zai yi annabci ba?
9Ku yi shela ga kagarun Ashdodda kuma ga kagarun Masar.“Ku tara kanku a tuddan Samariya;ku ga rashin jituwar da take a cikinta,da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.”
10“Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,”in ji Ubangiji,“sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.”11Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,“Abokin gāba zai ƙwace ƙasar,zai saukar da mafakarku,zai washe kagarunku.”12Ga abin da Ubangiji ya ce,“Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zakiƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya,haka za a ceci Isra’ilawa,masu zama a Samariyada kan gado kawaida kuma a ɗan ƙyalle a kan dogayen kujerunsu.13“Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki.14“A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta,zan hallaka bagadan Betel;za a yayyanka ƙahonin bagadanza su fāɗa ƙasa15Zan rushe gidan ranida na damina;gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe suhaka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,”in ji Ubangiji.