Amos2hau_bib

1Ga abin da Ubangiji ya ce,“Saboda zunubai uku na Mowab,har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.Gama ya ƙone ƙasusuwan sarkin Edomsuka zama sai ka ce toka.2Zan sa wuta a Mowabda za tă ƙone kagarun KeriyotMowab za tă gangara cikin hayaniya mai girmacikin kururuwar yaƙi da kuma ƙarar ƙaho.3Zan hallaka mai mulkintazan kuma kashe shugabanninta.”4Ga abin da Ubangiji ya ce,“Saboda zunubai uku na Yahuda,har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.Gama sun ƙi bin dokar Ubangijiba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba,domin allolin ƙarya sun ruɗe su,allolin da kakanninsu suka bauta.5Zan sa wuta a Yahudada za tă ƙone kagarun Urushalima.”

Hukunci a kan Isra’ila

6Ga abin da Ubangiji ya ce,“Saboda zunubai uku na Isra’ila,har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.Don sun sayar da adalai waɗandasuka kāsa biyan bashinsu.Sun kuma sayar da matalautawaɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.7Sun tattake kawunan matalautakamar yadda suke taka lakasuka kuma danne wa marasa galihu gaskiya.Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda,suna kuma ɓata sunana mai tsarki.8Suna kwanciya kurkusa da kowane bagadea kan tufafin da suka karɓe jingina.A gidajen allolinsusukan sha ruwan inabin da suka karɓo daga wurin waɗanda suka ci wa tara.
9“Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu,ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ulkuma mai ƙarfi kamar itacen oak.Na hallaka ’ya’yan itatuwansa daga sama,da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa.10Na fitar da ku daga ƙasar Masar,na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamadadon in ba ku ƙasar Amoriyawa.
11“Na kuma tā da annabawa daga cikin ’ya’yanku mazawaɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku.Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?”In ji Ubangiji.12“Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabikuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci.
13“Saboda haka, yanzu zan murƙushe kukamar yadda amalanke yakan murƙushe sa’ad da aka yi masa labtun hatsi.14Masu gudu da sauri ba za su tsira ba,masu ƙarfi ba za su iya yin amfani da ƙarfinsu ba,jarumi kuma ba zai iya ceton ransa ba.15’Yan baka ba za su iya dāgewa ba,masu saurin gudu ba za su tsira bamahayin dawakai kuma ba zai tsere da ransa ba.16Ko jarumawa mafi jaruntakaza su gudu tsirara a ranan nan,”in ji Ubangiji.