1 Tarihi26hau_bib
Matsaran ƙofofi
1Ɓangarorin Matsaran Ƙofofi su ne,Daga Korayawa, Meshelemiya ɗan Kore, ɗaya daga cikin ’ya’yan Asaf maza.2Meshelemiya yana da ’ya’ya maza. Zakariya ɗan fari, Yediyayel na biyu, Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu,3Elam na biyar, Yehohanan na shida da Eliyehoyenai na bakwai.4Obed-Edom shi ma yana da ’ya’ya maza. Shemahiya ɗan fari, Yehozabad na biyu, Yowa na uku, Sakar na huɗu Netanel na biyar,5Ammiyel na shida, Issakar na bakwai da Feyuletai na takwas. (Gama Allah ya albarkace Obed-Edom.)6Ɗan Obed-Edom, wato, Shemahiya shi ma yana da ’ya’ya maza, waɗanda suke shugabanni a cikin iyalin mahaifinsu, gama su jarumawa ne ƙwarai.7’Ya’yan Shemahiya maza su ne, Otni, Rafayel, Obed da Elzabad; danginsa Elihu da Shemahiya su ma jarumawa ne.8Ɗaukan waɗannan zuriyar Obed-Edom ne; su da ’ya’yansu maza da danginsu, jarumawa ne masu ƙarfin yin aiki. Zuriyar Obed-Edom, mutum 62 ne duka.9Meshelemiya yana da ’ya’ya maza da kuma ’yan’uwa, waɗanda jarumawa ne, su 18 ne duka.10Hosa dangin Merari yana da ’ya’ya maza. Shimri na fari (ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, mahaifinsa ya sa shi na fari),11Hilkiya ne na biyu, Tabaliya ne na uku sai kuma Zakariya na huɗu. ’Ya’ya da dangin Hosa su 13 ne duka.12Waɗannan ɓangarori na matsaran ƙofofi, ta wurin manyansu, suna da ayyukan yin hidima a haikalin Ubangiji, kamar yadda danginsu suke da shi.13Aka jefa ƙuri’u don kowace ƙofa bisa ga iyalansu, ƙarami da babba.14Ƙuri’a don Ƙofar Gabas ta fāɗo a kan Shelemiya. Sai aka jefa ƙuri’u don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai ƙuri’a ta ƙofar arewa ta fāɗo a kansa.15Ƙuri’a don Ƙofar Kudu ta fāɗo a kan Obed-Edom, ƙuri’a don ɗakin ajiya kuwa ta fāɗo a kan ’ya’yansa maza.16Ƙuri’u don Ƙofar Yamma da kuma Ƙofar Shalleket a hanyar bisa suka fāɗo a kan Shuffim da Hosa.
Aikin tsaro bisa ga mai tsaro.17Akwai Lawiyawa shida da suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu-biyu suke tsaron ɗakunan ajiya.18Game da filin waje ta yamma kuwa, akwai masu tsaro huɗu a hanya da kuma biyu a filinkansa.19Waɗannan su ne ɓangarori na matsaran ƙofofi waɗanda suke zuriyar Kora da Merari.