1 Tarihi25hau_bib
Mawaƙa
1Dawuda tare da shugabannin mayaƙa, suka keɓe waɗansu daga ’ya’yan Asaf, Heman da Yedutun don hidimar yin annabci, suna amfani da garayu, molaye da ganguna. Ga jerin mutanen da suka yi wannan hidima.2Daga ’ya’yan Asaf, Zakkur, Yusuf, Netaniya da Asarela. ’Ya’yan Asaf sun kasance a ƙarƙashin kulawar Asaf, wanda ya yi annabci a ƙarƙashin kulawar sarki.3Game da Yedutun kuwa, daga ’ya’yansa maza. Gedaliya, Zeri, Yeshahiya, Shimeyi, Hashabiya da Mattitiya, su shida ne duka, a ƙarƙashin kulawar mahaifinsu Yedutun, wanda ya yi annabci, yana amfani da garaya a yin godiya da yabon Ubangiji.4Game da Heman kuwa, daga ’ya’yansa maza. Bukkiya, Mattaniya, Uzziyel, Shebuwel, Yerimot; Hananiya, Hanani, Eliyata, Giddalti, Romamti-Ezer, Yoshbekasha, Malloti, Hotir da Mahaziyot.5Dukan waɗannan ’ya’yan Heman ne mai duba na sarki. An ba shi su ta wurin alkawarin Allah don yă ɗaukaka shi. Allah ya ba Heman ’ya’ya maza goma sha huɗu da ’ya’ya mata uku.6Dukan waɗannan mutane suna a ƙarƙashin kulawar mahaifansu don kaɗe-kaɗe da bushe-bushe a cikin haikalin Ubangiji, da ganguna, molaye da garayu, don hidima a gidan Allah. Asaf, Yedutun da Heman suna ƙarƙashin kulawar sarki.7Da su da danginsu, dukansu su 288 ne kuma horarru da ƙwararru ne a kaɗe-kaɗe da bushe-bushe domin Ubangiji.8Baba ko yaro, malami ko ɗalibi, duk suka jefa ƙuri’a saboda ayyukan da za su yi.9Ƙuri’a ta fari, wadda take don Asaf, ta fāɗo a kan Yusuf, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta biyu a kan Gedaliya, danginsa da ’ya’yansa maza, 1210ta uku a kan Zakkur, ’ya’yansa da danginsa, 1211ta huɗu a kan Izri, ’ya’yansa maza da danginsa, 1212ta biyar a kan Netaniya, ’ya’yansa maza da danginsa, 1213ta shida a kan Bukkiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 1214ta bakwai a kan Yesarela, ’ya’yansa maza da danginsa, 1215ta takwas a kan Yeshahiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 1216ta tara a kan Mattaniya, ’ya’yansa maza da danginsa, 1217ta goma a kan Shimeyi, ’ya’yansa maza da danginsa, 1218ta goma sha ɗaya a kan Azarel, ’ya’yansa maza da danginsa, 1219ta goma sha biyu a kan Hashabiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 1220ta goma sha uku a kan Shubayel, ’ya’yansa maza da danginsa, 1221ta goma sha huɗu a kan Mattitiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 1222ta goma sha biya a kan Yeremot, ’ya’yansa maza da danginsa, 1223ta goma sha shida a kan Hananiya, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 1224ta goma sha bakwai a kan Yoshbekasha, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 1225ta goma sha takwas a kan Hanani, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa 1226ta goma sha tara a kan Malloti, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 1227ta ashirin a kan Eliyata, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 1228ta ashirin da ɗaya a kan Hotir, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 1229ta ashirin da biyu a kan Giddalti, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 1230ta ashirin da uku a kan Mahaziyot, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa, 1231ta ashirin da huɗu a kan Romamti-Ezer, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa 12.No translations available.