Zefaniya2hau_bib
1Ku tattaru, ku tattaru,Ya ku al’umma marar kunya,2kafin ƙayyadadden lokacin nan yă zoranan nan kuma ta share ku kamar ƙaiƙayikuma kafin fushi mai tsanani na Ubangiji yă auko muku,kafin ranar fushin Ubangiji ta auko muku.3Ku nemi Ubangiji, dukanku ƙasashe masu tawali’u,ku da kuke yin abin da ya umarta.Ku nemi adalci da tawali’u;mai yiwuwa ku sami mafaka a ranar fushin Ubangiji.