1Maganar Ubangiji da ta zo wa Zefaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda.
Gargaɗi a kan hallaka mai zuwa
2“Zan hallaka komea fuskar duniya,”in ji Ubangiji.3“Zan hallaka mutane da dabbobi;zan kuma hallaka tsuntsayen samada kifayen teku,da gumakan da suke sa mugaye su yi tuntuɓe.”“Sa’ad da zan kawar da mutum daga fuskar duniya,”in ji Ubangiji.4“Zan miƙa hannuna gāba da Yahudada kuma dukan mazaunan Urushalima.Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri,da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,5waɗanda suka rusuna a kan rufin ɗakidon su yi sujada ga rundunar taurari.Waɗanda suka rusuna suka kuma yi rantsuwa da sunan Ubangijisuke kuma rantsuwa da sunan Molek.6Waɗanda suka juya daga bin Ubangiji,ba sa kuma neman Ubangiji ko su nemi nufinsa.”7Ku yi shiru a gaban Ubangiji Mai Iko Duka,gama ranar Ubangiji ta yi kusa.Ubangiji ya shirya hadaya;ya kuma tsarkake waɗanda ya gayyato.8“A ranar hadayar Ubangijizan hukunta sarakunada kuma ’ya’yan sarakunada duk waɗanda suke sanyeda rigunan ƙasashen waje.9A wannan rana zan hukuntadukan waɗanda suke kauce taka madogarar ƙofa,waɗanda suke cika haikalin allolinsuda rikici da ruɗu.10“A wannan rana,”in ji Ubangiji,“Za a ji kuka daga Ƙofar Kifi,kururuwa daga Sabon Mazauni,da kuma amo mai ƙarfi daga tuddai.11Ku yi kururuwa, ku da kuke zaune a yankin kasuwa;za a hallaka dukan ’yan kasuwanku,dukan waɗanda suke kasuwanci da azurfa za su lalace.12A wannan lokaci zan bincike Urushalima da fitiluin kuma hukunta waɗanda ba su kula ba,waɗanda suke kamar ruwan inabin da aka bar a ƙasan tukunya,waɗanda suke tsammani, ‘Ubangiji ba zai yi kome banagari ko mummuna.’13Za a washe dukiyarsu,a rurrushe gidajensu.Za su gina gidajeamma ba za su zauna a ciki ba;za su shuka inabiamma ba za su sha ruwansa ba.”14Babbar ranar Ubangiji ta yi kusa,ta yi kusa kuma tana zuwa da sauri.Ku saurara! Kukan ranar Ubangiji za tă yi zafi,za a ji kururuwan jarumi a can.15Ranan nan za tă zama ranar fushi,rana ce ta baƙin ciki da azaba,rana ce ta tashin hankali da lalacewa,ranar duhu baƙi ƙirin,ranar gizagizai da baƙin duhu,16rana ce ta busa ƙaho da kururuwar yaƙigāba da birane masu mafaka,da kuma kusurwar hasumiyoyi.17“Zan kawo baƙin ciki a kan mutaneza su kuma yi tafiya kamar makafi,domin sun yi wa Ubangiji zunubi.Za a zubar da jininsu kamar ƙurakayan cikinsu kuma kamar najasa.18Azurfarsu ko zinariyarsuba za su iya cetonsu baa ranar fushin Ubangiji.”A cikin zafin kishinsaza a hallaka dukan duniyagama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniyanan da nan.