1Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara;Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari.Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan samayana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa.2Gumaka suna maganganun ruɗu,masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya,suna faɗa mafarkan ƙaryasuna ba da ta’aziyyar banza.Saboda haka mutane suna yawo kamar tumakiwaɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi.3“Ina fushi da makiyayan,zan kuma hukunta shugabannin;gama Ubangiji Maɗaukaki zai lurada garkensa, wato, gidan Yahuda,zai kuma sa su zama kamar doki mai fariya cikin yaƙi.4Daga Yahuda dutsen kusurwa zai fito,daga gare shi za a samu abin kafa tenti,daga gare shi za a sami bakan yaƙi,daga gare shi za a sami kowane mai mulki.5Tare za su zama kamar mutane masu ƙarfisuna tattake lakar tituna a cikin yaƙi.Domin Ubangiji yana tare da su,za su yi faɗa su kuma yi nasara a kan masu yaƙi a kan dawakai.6“Zan ƙarfafa gidan Yahudain kuma ceci gidan Yusuf.Zan maido da sudomin ina jin tausayinsu.Za su zama kamarban taɓa ƙinsu ba,gama ni ne Ubangiji Allahnsuzan kuma amsa musu.7Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi,zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi.’Ya’yansu za su gani su yi murna;zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji.8Zan ba da alamain kuma tattara su.Ba shakka zan fanshe su;za su yi yawa kamar yadda suke a dā.9Ko da yake na warwatsa su cikin mutane,duk da haka a can ƙasashe masu nisa za su tuna da ni.Su da ’ya’yansu za su rayu,za su kuwa komo.10Zan komo da su daga Masarin kuma tattara su daga Assuriya.Zan kawo su Gileyad da Lebanon,har wuri yă kāsa musu.11Za su ratsa cikin tekun wahala;zan kwantar da raƙuman tekudukan zurfafan Nilu kuma za su bushe.Za a ƙasƙantar da Assuriya,sandar sarautar Masar kuma za tă rabu da ita.12Zan ƙarfafa su a cikin Ubangijikuma a cikin sunansa za su yi tafiya,”in ji Ubangiji.