Titus1hau_bib
1Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah2duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,3da lokacin da Allah ya zaɓa ya cika sai ya bayyana maganarsa a sarari ta wurin wa’azin da aka danƙa mini amana ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu,4Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya.
Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu, su kasance tare da kai.
Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu, su kasance tare da kai.