Waƙar Waƙoƙi7hau_bib
1Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne,Ya diyar sarki!Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja,aikin hannun gwanin sassaƙa.2Cibinki kamar kwaf neda bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba.Kwankwasonki ya yi kamar damin alkamawanda furen bi-rana ya kewaye.3Nonanki sun yi kamar bareyi biyu,tagwayen barewa.4Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa.Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbonkusa da ƙofar Bat Rabbim.Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanonwadda take duban Damaskus.5Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel.Gashinki ya yi kamar shunayya;yakan ɗauke hankalin sarki.6Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi,Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo!7Tsayinki ya yi kamar itacen dabino,kuma nonanki sun yi kamar ’ya’yan itace.8Na ce, “Zan hau itacen dabino;zan kama ’ya’yansa.”Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa,ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa,9kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau.ƘaunatacciyaBari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena,yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora.10Ni ta ƙaunataccena ce,kuma sha’awarsa domina ne.11Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari,bari mu kwana a ƙauye.12Bari mu tafi gonar inabi da sassafedon mu ga ko kuringar ta yi ’ya’ya,ko furanninsu sun buɗe,ko rumman sun yi fure,a can zan nuna maka ƙaunata.13Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu,a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi,sabo da tsoho,da na ajiye dominka, ƙaunataccena.